Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta yi karin bayani kan maharin Louisiana

Mahukuntan Amurka sun ce, dan bindigar da ya hallaka ‘yan sanda uku a birnin Baton Rouge na jihar Louisiana, tsohon sojin ruwan kasar ne da ya taba aiki a Iraqi.

Shugaban Amurka Barack Obama ya yi tir da harin wanda ya yi sanadiyar mutuwar 'yan sandan Baton Rogue na Louisiana
Shugaban Amurka Barack Obama ya yi tir da harin wanda ya yi sanadiyar mutuwar 'yan sandan Baton Rogue na Louisiana REUTERS/Joshua Roberts
Talla

Mahukuntan sun bayyana Gavin Eugene Long mai shekaru 29 da haihuwa kuma dan asalin Kansas da ke jihar Missouri a matsayin wanda ya kashe ‘yan sandan.

Sai dai binciken da aka gudanar a kansa ya nuna cewa, babu wani babban laifi da ya taba aikatawa a baya a jiharsa ta Missouri.

Kafofin yada labaran Amurka sun ce, har yanzu an gaza gano yadda matashin ya kaddamar da harin kan ‘yan sandan na Baton Rouge.

Tun lokacin da wani dan sanda ya harbe wani matashi bakar fata mai suna Alton Sterling har lahira ne, birnin ya zama wani dandalin zanga-zangar adawa da kisan da ake yi wa bakaken fata a Amurka.

Rahotanni sun ce gabanin kaddamar da harin na jiya, Long wanda shi ma bakar fata ne, ya fitar da fayafayen bidiyo a shafin intanet, inda ya yi korafi kan yadda ‘yan sanda ke cin zarafin bakaken fata Amurkawa, kana ya buka ce da su da su mayar da martini kan abinda ake yi musu.

Tuni dai aka kashe matashin a yayin arangama da ya jami’an ‘yan sandan na Lousiania.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.