Hari da bindiga ya hallaka mutane 5 a Amurka
An kai harin bindiga a jihohin Louisiana da Florida a yau lahadi, mutane 5 aka tabbatar da mutuwarsu, 3 daga cikinsu ‘yan sanda ne dake bakin aiki a yankin Baton Rouge, akwai kuma wasu mutane 4 da suka sami rauni sanadiyar harin na yau lahadi.
Wallafawa ranar:
Hakazalika Wani dan bindiga ya buda wuta tare da kashe mutane 2 a wani asibiti da ke Florida.
‘Yan sanda sun ce daya daga cikin mamatan wata tsohuwa ce da ke jinya a asibitin, yayin da shi kuma daya aka ce ma’aikaci ne a wannan asibitin.
Wata guda kenan da wani dan bindiga ya bude wuta a gidan rawar masu auren jinsi inda ya kuma hallaka 49 daga cikinsu a birnin Orlando dake jahar ta Florida, al’amarin da ya kasance hari mafi muni a tarihin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu