Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiya na ci gaba da daukan mataki kan juyin mulki

Gwamnatin Turkiya na ci gaba da daukan tsauraran matakai kan wadanda ta ke zargi da yunkurin kifar da mulkin shugaba Reccep Tayyip Erdogan, yayin da Fetuhullah Gulen ya ce, baya fargaban Amurka ta tasa keyarsa zuwa Turkiya saboda zargin sa da hannu a juyin mulkin da bai yi nasara ba.

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan da malamin Islama  Fethullah Gülen da ke zaune a Amurka
Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan da malamin Islama Fethullah Gülen da ke zaune a Amurka AFP PHOTO / THIERRY CHARLIER / ZAMAN DAILY / SELAHATTIN SEVI
Talla

Kawo yanzu mahukuntan Turkiya sun tsare mutane fiya da dubu 7 da 500 tare da sallamar jami’an gwamnati kusan dubu 9 saboda zargin su da hannu wajen kitsa juyin mulkin.

Erdogan ya zargi malamin Islaman nan da ke zauna a Amurka, Fethullah Gulen da kokarin kifar da gwamnatinsa, abinda da ya sa ya bukaci Amurkan ta tasa keyarsa zuwa Turkiya.

Sai dai malamin mai shekaru 75 ya ce, baya fargaban a maido da shi Turkiyar kuma ya musanta zargin da ake yi masa.

Gulen dai na da magoya baya a bangarori daban-daban na Turkiya, kama daga kafafan yada labarai da aikin ‘yan sanda da bangaren shari’a, abinda yasa Erdogan ke zargin sa da tafiyar da wata gwamnati cikin gwamnati.

A bangare guda, a jiya litinin ne, tsohon kwamandan sojin saman kasar, Akin Ozturk ya bayyana a gaban kotu a cikin wani yanayi na tagayyara, ga kuma bandeji a kunnansa, inda ya musanta jagorantar yukunkurin juyin mulkin wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 300.

Kamfanin dillancin labaran kasar, ya rawaito Janar Ozturk na cewa, ba shi da hannu a lamarin, kana bai san wanda ya kitsa juyin mulkin ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.