MDD ta yi gargadin amfani da Yunwa a yaki
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi cewa miliyoyin mutane na gab da fadawa cikin wani hali sakamon rashin abinci a kasashen da ake amfani da yunwa wajen cimma manufar yaki.
Wallafawa ranar:
Sama da mutane miliyan 50 dake zaune a yankunan 17 na kasashen duniya majalisar tace na rayuwa cikin mastananci hali, musamman a Syria da Yemen da Najeriya.
A kasar Yemen kawai mutane miliyan 14, sama da rabin alummar kasar ke bukatar agajin gaggawa.
Yayin da a Syria ake da mutane kusan miliyan 9, sai Najeriya da rikicin Boko Haram ya tagayara rayuwar miliyoyin mutane da rayuwarsu ke cikin kunci, musamman kanana yara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu