Isa ga babban shafi
Najeriya

Yunwa na kashe mutane a kullum a Borno

Akalla mutane 10 ke mutuwa a kowacce rana saboba tsananin yunwa a sansanin ‘yan gudun hijirar Boko Haram da ke arewa maso gabashin Najeriya.

'Yan gudun hijirar Boko Haram na mutuwa saboda yunwa a sansaninsu da ke Banki na Borno
'Yan gudun hijirar Boko Haram na mutuwa saboda yunwa a sansaninsu da ke Banki na Borno REUTERS/African Union-United Nations
Talla

Wani dan kato da gora da wani soja sun bayyana wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, ana samun asarar rayukan ne a sansanin garin Banki mai tazarar kilomita 130 daga babban birnin Maiduguri na jihar Borno.

Rahotanni sun ce, maza da mata da kananan yara na cikin wadanda musibar ke sha  a kullum tun lokacin da aka bude sansanin watanni uku da suka gabata.

Dan kato da goran da kuma sojan sun ce, ya zuwa ranar Larabar da ta gabata, sun kirga kaburbura 376 na mutanen da wannan ibtila’in ya cika da su, kuma an binne su ne a makabartar Bulachira.

Wannan al’amarin dai ya kara nuna yadda ake fama da matsalar karancin abinci a yankin tafkin Chadi saboda rikicin Boko Haram wanda ya tsananta shekaru bakwai da suka gabata.

A watan Mayun da ya gabata ne majalisar dinkin duniya ta ce, kimanin mutane miliyan 9 da dubu 200 ke bukatar abinci a yankin tafkin Chadi da yada hada kan iyakokin Najeriya da Chadi da Kamaru da Nijar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.