Isa ga babban shafi
Amurka

Hillary da Obama ne suka kafa Kungiyar IS inji Trump

Dan takaran shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Republican, Donald Trump ya ce ‘yar takaran Shugabancin karkashin jamiyyar Democrat tare da Shugaba mai ci yanzu su ne suka kafa kungiyar IS ta masu ikirarin jihadi.

Hoton Donald Trump da Hillary Clinton
Hoton Donald Trump da Hillary Clinton RFI/ REUTERS/Mike Segar/Whitney Curtis
Talla

Kafin wannan furuci  Donald Trump ya yi wani shagube dake bukatar Amurkawa masu dauke da bindiga su dauki mataki kan Hillary Clinton, kalaman da suka sa jami’an tsaro suka yi masa tambayoyi.

Da yake jawabi ga magoya bayan sa a gangami da aka yi a Fort Lauderdale, Florida   ya ce lallai kungiyar IS ta masu ikirarin jihadi na girmama Shugaba Barack Obama.

Donald Trump wanda ya sha yin kalamai masu nauyi yayin wannan yakin neman zabe da ake yi.

Uwargida Hillary Clinton ta fadi a jawabin ta ga magoya bayan ta a Des Moines, Iowa cewa abokin takaran na ta soki burutsu kawai yake yi.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.