Mayakan IS sun sace mutane 2,000
Yan tawayen Syria dake samun goyon bayan kasashen yamma sun sanar da datse duk wata hanya da mayakan ISIL za su bi su ketara zuwa nahiyar turai.
Wallafawa ranar:
Lamarin na zuwa ne bayan da ‘yan tawayen Syrian da suka kunshi Kurdawa da larabawa suka bayyana cewa mayakan na ISIL sun sace mutane akalla 2,000 don yin garkuwa da su yayin da mayakan suka tsere daga arewacin birnin Manbij.
Mai Magana da yawun yan tawayen Sharfan Darwish ya ce yanzu haka sun kwace ikon yawancin yankunan birnin na Manbij daga hannun mayakan na IS.
Rahotanni sun ce an ga sama da motoci dari biyar makare da mutane na barin Birnin na Manbij zuwa Jarabulus da ke iyaka da Turkiyya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu