Isa ga babban shafi
saudiya

Saudiya ta mayar wa Iran martani kan aikin hajji

Saudi Arabia ta mayar da martani mai zafi kan kalaman shugaban addinin Iran Ayatullah Ali Khamenei na cewar musulumin duniya su kalubalanci yadda Saudiyar ke gudanar da ayyukan hajji.

Dandazon al'ummar musulmi da ke ibada a lokacin aikin hajji a Saudiya
Dandazon al'ummar musulmi da ke ibada a lokacin aikin hajji a Saudiya Flickr user 'transposition'
Talla

Shugaban malaman Saudiya, Aldulaziz Al-Sheikh ya bayyana Iraniyawan a matsayin wadanda ba musulmai ba saboda yadda suke kyamar Saudiyyan da mabiya Sunnah.

A nashi bangaren, Yarima mai jiran gado Mohammed bin Nayef ya ce, Saudiya ta dauki duk matakan da suka dace wajen kare lafiyar mahajjata da kuma inganta jin dadinsu ta hanyar samar musu da masaukai na zamani da kuma tsaro.

Nayef ya ce, sun ki amince wa da bukatar Iran na gudanar da zanga-zanga a lokacin aikin hajji, daya daga cikin dalilan da ya hana mahajjantan kasar zuwa aikin hajjin bana.

Alhazan Iran 464 suka mutu a hadarin bara, kuma ga alama cacar baki tsakanin bangarorin biyu ba zai kau ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.