Isa ga babban shafi
EU

EU ta goyi bayan aiwatar da yarjejeniyar Paris

Majalisar dokokin kasashen Turai ta goyi bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar magance dimamar yanayi da aka cimma a birnin Paris na Faransa, bayan ta kada kuri’ar da ta samu halartar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon a wannan Talata. 

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya  Ban-Ki-Moon a majalisar dokokin kasashen Turai da ta kada kuri'ar yarjejeniyar Paris a ranar Talata a birnin Strasbourg
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban-Ki-Moon a majalisar dokokin kasashen Turai da ta kada kuri'ar yarjejeniyar Paris a ranar Talata a birnin Strasbourg REUTERS/Vincent Kessler
Talla

Matakin da majalisar dokokin ta dauka zai taimaka wajen gaggauta aiki da yarjejeniyar  a duk fadin duniya.

Mambobin majalisar 610 ne suka goyi bayan rattaba hannun, in da 38 suka ki amincewa da haka, yayin da 31 suka kaurace wa kada kui’ar.

Sakamakon kuri’ar dai na nufin cewa, nan da ranar jumma’a mai zuwa, kasashen na Turai za su gabatar da rattaba hannun a gaban Majalisar Dinkin Duniya, abin da zai tinzira sauran kasashen duniya wajen aiwatar da yarjejeniyar ta rage fitar da yaki mai guba.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon, ya yi jawabi a gaban mambobin majalisar fiye da 700 a birnin Strasbourg, in da ya ce musu, suna da damar kafa tarihi ta hanyar jan ragama don samar wa duniya kyakkyawar makoma.

Tuni dai Amurka da China da India da ke kan gaba wajen fitar gurbataccen hayaki suka rattaba hannu kan yarjejeniyar wadda aka cimma a watan Disamban bara, yayin da ake bukatar rattaba hannun daga kasashe 55 da ke fitar da kashi 55 na hayakin a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.