Isa ga babban shafi
Amurka

Clinton na ci gaba da bai wa Trump tazara

Yayin da ya rage kusan makwanni biyu a gudanar da zaben shugaban kasar Amurka, 'yar takarar jam’iyyar Democrat Hillary Clinton na ci gaba da bai wa Donald Trump na Jam’iyyar Republican tazara a jihohin da ake ganin za su fafata.

Hillary Clinton na ci gaba da bai wa  Donald Trump tazara a fafatukar neman maye gurbin shugaba Obama na Amurka
Hillary Clinton na ci gaba da bai wa Donald Trump tazara a fafatukar neman maye gurbin shugaba Obama na Amurka REUTERS/Mike Blake
Talla

Tashar talabijin din ABC ta ruwaito cewa, Clinton na gaban Trump da kashi 50 na kuri’un jin ra’ayoyin jama’a, yayin da Trump ke da kashi 38 cikin 100.

Wannan shi ne karo na farko da Clinton ta samu wannan farin jini tun bayan kaddamar da yakin neman zaben ta don maye gurbin shugaba Barack Obama.

A bangare daya kuma, an sake samun wata mata da ta fito fili inda ta ce, Donald Trump yaci zarafin ta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.