Isa ga babban shafi
Turkiya-EU

Erdogan na zargin Turai da mara wa Kurdawa

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan, ya zargi kasahsen Turai da nuna goyon baya ga Kurdawa 'yan ta’adda da ke ci gaba da kai hare-hare a cikin kasar. 

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan na ci gaba da daukan tsauraran matakai kan wadanda ake zargi da kokarin kifar da gwamnatinsa
Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan na ci gaba da daukan tsauraran matakai kan wadanda ake zargi da kokarin kifar da gwamnatinsa Sputnik
Talla

Erdogan ya ce, kungiyar Kurdawa ta PKK ta hallaka akalla jami’an tsaro 800 da kuma fararen hula 300 a hare-haren da take kaiwa.

Yayin da yake jawabi a jami’ar Santanbul, shugaba Erdogan da ya kama wadanda ake zargi da yunkurin juyin mulki cikin su har da shugabannin jam’iyyar Kurdawan ya ce, bai damu kan cewa kasashen Turai su kira shi mai mulkin kama karya ba, muddin yana yin abin da jama’arsa ke so.

Erdogan ya kara da cewa, nuna goyan baya ga Kurdawan, tamkar taimaka wa aikin ta’addanci ne.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.