Isa ga babban shafi
Amurka

Trump zai fara da korar Bakin Haure Miliyan Uku

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya ce abu na farko da zai fara aiwatarwa da zaran an mika masa mulki,  shi ne ya hanzarta fatattakan bakin haure kusan miliyan uku da suka yi kaka-gida a Amurka.

Zababben Shugaban kasar Amurka Donald Trump
Zababben Shugaban kasar Amurka Donald Trump Reuters
Talla

Donald Trump wanda ake tattaunawa da shi a gidan Talabijin na CBS yau Lahadi,  ya tabbatar cewa da zaran ya kama aiki to kuwa bakin haure za su gane kurensu.

A cewar sa abin da zai yi shi ne ya tantance domin gano masu laifi, da ‘yan kungiyoyin tsiya, da dillalan miyagun kwayoyi, da yawansu ya kai sama da Miliyan biyu domin a iza keyarsu su koma kasashen na asali.

Sannan shugaban mai jiran gado ya nanata aniyarsa ta gina ganuwa akan iyakar Amurka da Mexico kamar yadda ya ta fada a yakin neman zaben shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.