Isa ga babban shafi
Brazil

Bankin Brazil zai kori dubban ma’aikata

Bankin Gwamnatin kasar Brazil ya sanar da shirin yin tankade da rairaya na ma’aikata dubu 18, tare da rufe rassan Bankin 400 a fadin kasar.

Shugaban Brazil Michel Temer
Shugaban Brazil Michel Temer REUTERS/Ueslei Marcelino
Talla

A cewar Hukumomin Bankin za a rufe rassansa 400 domin tanadin kudade da suka kai kudin kasar Rais miliyan 750.

Karkashin tankade da rairayan dai an tsara rage akalla ma’aikata 9,300 ne daga cikin ma’aikata 109,159.

Sai dai Bankin ya ce ya tanadi albashi na kimanin watanni 10 zuwa 15 ga dukkan ma’aikacin da zaa raba da aikin Bankin.

Sannan Bankin ya ce ya rage lokacin ayyukan bankin daga sa’o’i 8 zuwa shida domin a yi tsimin kudade da ake kashewa.

Wasu bayanai sun nuna hannun jari a Bankin ya sami tagomashi bayan samun wannan labari.

Kasar Brazil na fama ne da komadan tattalin arziki kuma masu hasashe na ganin watakila tattalin arzikin kasar ya murmure daga badi.

Matsalar tattalin arziki na daga cikin dalilan da suka kawo karshen mulkin Dilma Rousseff.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.