Isa ga babban shafi
Haiti

Moise ya lashe zaben Haiti

Hukumar Zaben Haiti ta ce Dan Kasuwa Jovenel Moise da ke samun goyan bayan tsohon shugaban kasa Michel Martelly ya lashe zaben kasar da kuri’u sama da kashi 55.

Jovenel Moïse ya lashe zaben Haiti
Jovenel Moïse ya lashe zaben Haiti HECTOR RETAMAL / AFP
Talla

Jami’in gudanar da zaben Uder Antoine ya ce Moise ya doke Jude Celestin na Jam’iyyar LAPEH da ya zo na biyu da kashi kusan 20, yayin da Moise Jean Charles ya zo na uku da kasha 11.

Dokar kasar ta bai wa dan takarar da bai gamsu da sakamakon ba ya ruga kotu domin kalubalantar sakamakon.

Moise dan kasuwa mai shekaru 48 bai taba rike wani mukamin gwamnati ba, amma ya sha alwashin habaka kasar.

‘Yan takara 27 suka fafata a zaben inda hudu daga cikinsu suka yi gaggawar sanar da samun nasara a zagayen farko kafin sanar da sakamakon a hukumance.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.