Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya soke kera jiragen Air Force One

Shugaban Amurka mai jiran gado, Donald Trump ya soke umarnin kera jiragen shugaban kasar da ake kira Air Force One saboda abin da ya kira tsananin tsadarsu.

Jirgin Air Force One na shugaban kasar Amurka
Jirgin Air Force One na shugaban kasar Amurka REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

An dai bayar da kwangilar kera jiragen ne akan kudi Dala biliyan 3 ga kamfanin Boeing don sanya musu kayan alatu na zamani nan da shekarar 2024.

A sakon da ya aike ta kafar Twitter, Trump ya ce, kamfanin Boeing na kera jirgin Air Force One kirar 747 amma farashinsu ya zarce Dala biliyan 4, saboda haka an soke kwangilar.

Matukar dai Trump bai lashe wa’adi na biyu a shekarar 2020 ba, to lallai ba zai samu damar shiga sabbin jiragen na shugaban kasar ta Amurka ba, lura da cewa za a fara amfani da su ne a shekarar 2024.
 

A cikin watan Janairun badi ne, Mr. Trump zai karbi mulki daga hannun shugaba Barack Obama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.