Isa ga babban shafi
Amurka

Bukatar sake kidaya kuri'u damfara ce inji Trump

Zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana kira da wasu suka yi na sake kidayar kuri’u a matsayin damfara.

Zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump.
Zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump. REUTERS/Carlo Allegri/File Photo
Talla

Mista Trump ya ce bai ga bukatar yin hakan ba ganin ko abokiyar takarar sa Hillary Clinton ta riga ta amince da shan kaye a zaben.

Kalaman Trump ya biyo bayan sanarwar da jam'iyyar Green Party ta yi inda ta bukaci sake kidayan kuri'u don kawar da zargin tafka magudi a zaben shugabancin kasar da Donald Trump ya lashe.

Jam’iyyar ta Green Party ta nemi a sake kidayar kuri'un zaben jihar Wisconsin inda Trump ya yi nasara da 'yar tazara,

Sakamakon Zaben Amurka dai ya nuna cewar Hillary Clinton
Clinton ta samu kuri’u miliyan 64 da yan kai yayin da Trump ya samu kuri’u miliyan 62

Wannan shine karo na biyu a cikin wannan karnin da Yan Jam’iyyar Dimokrat ke samun yawan kuri’u amma kuma suke rasa kujerar shugabancin kasar.

A shekara ta 2000 Al Gore ya zarce George Bush da kuri’u dubu dari biyar da arba’in da hudu amma kuma bai samu kujerar shugabancin kasar ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.