Isa ga babban shafi
Amurka

Trump zai yi watsi da yarjejeniyar Fasifik

Zababben Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar soke yarjejeniyar kasuwanci ta kasashen Fasific da ake kira TPP a ranar farko da ya kama aiki wacce ta kunshi kasashe 12 da suka sanya wa hannu.

Donald Trump ya ce ci gaban Amurka ne farko a mulkin shi
Donald Trump ya ce ci gaban Amurka ne farko a mulkin shi Reuters
Talla

Yin watsi da yarjejeniyar na cikin muradun shugaban mai jiran gado guda shida da ya ta fada a yakin neman zaben shi mai taken ci gaban Amurka ne farko.

Yarjejeniyar TTP ta kunshi kasashen da suka mallaki kashi 40 na harkokin kasuwancin duniya.

A wani faifan bidiyo da ya rabawa manema labarai, Trump ya bayyana cewar ya shaidawa kwamitin karban mulkin da ya nada ya tattara dokokin da za su dauki mataki akan su ranar farko da kama aiki dan dawo da martabar Amurka.

Trump ya danganta yarjejeniyar kasuwancin ta kasashen Fasific a matsayin mai cike da hadari ga Amurka inda ya ce zai musanya yarjejeniyar da wasu sabbin matakan da za su taimakawa Amurka wajen dawo da ayyuka da kuma masana’antu kasar.

Sannan Trump ya ce zai janye dokokin da suka takaita samun makamashi a Amurka cikin su har da makamashin Shell da kuma gawayi wadanda ke samar da miliyoyin ayyuka da ke biya da tsoka.

Tuni dai Firaministan Japan Shinzo Abe ya bayyana cewar yarjejeniyar TPP ba ta da wani amfani idan har Amurka ta fice.

A ranar 20 ga watan Janairu ne Donald Trump zai kama aiki a fadar White House.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.