Isa ga babban shafi
Amurka

Obama ya kammala ziyarar karshe a matsayin shugaban Amurka.

Shugaban Kasar Amurka Barack Obama ya kawo karshen ziyarar sa zuwa kasashen duniya a matsayin shugaban kasa bayan kwashe shekaru 8 ana damawa da shi.

Obama ya kammala ziyarar karshe a matsayin shugaban Amurka.
Obama ya kammala ziyarar karshe a matsayin shugaban Amurka. Clemens BILAN / AFP
Talla

A yayin jawabinsa na karshe a yayin wannan ziyarar, Obama ya bai wa wanda zai gaje shi Donald Trump shawarar hada kai da kasashen duniya domin cimma muradun Amurka.

Shugaban ya kuma yi karin bayani kan inda zai nufa da zarar ya sauka daga mulkin Amurka, Obama dai ya ce idan ya mika mulki a watan Janairu zai dauki lokaci don ya huta da iyalan sa kana ya yi rubuce rubuce da kuma nazari.

Firaministan Australia da na Canada kasashen da Obama ya karkare da ziyararsa sun bayyana damuwar su na rabuwa da shugaban inda suka ce lallai za suyi kewar sa.

Obama ya kasance shugaban kasar Amurka bakar fata na farko da aka taba samu a tarihin kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.