Isa ga babban shafi
EU

EU na taron kwana guda a Brussels

Kungiyar kasashen Turai na gudanar da wani taro a birnin Brussels don tattauna kan matsalar bakin haure da ficewar Birtaniya da kuma tsawaita takunkumin karayar tattalin arziki da ta kakaba wa Rasha.

Theresa May ta Birtaniya da shugabannin kasashen Turai
Theresa May ta Birtaniya da shugabannin kasashen Turai REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Taron na kwana guda, zai kuma mayar ta hanakali kan dangantakar nahiyar Turai da Turkiya da kuma yakin basasar da ake fama da shi a Syria.

Sai dai bayan wani dan lokaci, shugabannin Turai 27 za su kebe don cin abincin dare ba tare da Firaministan Birtaniya ba Theresa May, in da za su tattaunawa kan ficeawr kasarta baki daya.

A yayin cin abincin, shugabannin za su cimma matsaya don tabbatar da wakilansu a batun ficewar Birtaniyar daga Turai.

A bangare guda, ana saran shugabannin na Turai za su tsawaita takunkumin da suka kakaba wa Rasha saboda mamayar da ta yi wa yankin Cremea na Ukraine.

To sai dai a dai dai lokacin da shugabannin za su tsawaita takunkumi kan Syria, sabani ya kaure a tsakanisu, in da wasu ke ganin ya dace a sake kakabawa Rasha wani sabon takunkumin saboda hare-haren da ta kai wa kan fareran hula a Aleppo.

Kazalika taron zai mayar da hanakali kan karfafa yarjejeniyar kungiyar kasashen Turai da Turkiya ta magance kwararar ‘yan gudun hijira.

Ana kuma kyautata azaton taron zai sanar da bayar da tallafi ga Jamhuriyar Nijar sakamakon rawar da kasar ke takawa wajen dakile ‘yan gudun hijira da ke ratsawa ta Libya zuwa Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.