Rasha-Turkiya
An kashe jakadan Rasha a Turkiya
Wani harin bindiga da aka kaddamar a birnin Ankara, ya yi sanadiyar mutuwar jakadan Rasha a Turkiya.
Wallafawa ranar:
Talla
Kafofin yada labaran Turkiya sun ce, dan bindigan ya harbi Andrei Karlov ne a baya kuma a daidai lokacin da ya ke gabatar da jawabi a wani bikin baje kolin hotuna.
Jama'a da dama sun jikkata sakamakon harin wanda aka kai bayan kwana guda da gudanar da wata zanga-zangar adawa da matakin Rasha na aikewa da sojojinta zuwa Syria mai fama da rikici.
Tuni dai Amurka ta yi Allah-wadai da harin wanda ya yi sanadiyar mutuwar jakadan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu