Isa ga babban shafi
Amurka-Syria

Rundunar kawance ta kashe fararen hula 188

Rundunar Sojin Amurka ta bayyana cewa, akalla fararen hula 188 ne aka kashe a hare-haren hadin gwiwa da kasar ta jagoranta tun daga shekarar 2014 don kakkabe mayakan IS a Syria da Iraqi.

Hare haren rundunar hadin gwiwa karkashin Amurka sun hallaka fararen hula da dama a Syria da Iraqi
Hare haren rundunar hadin gwiwa karkashin Amurka sun hallaka fararen hula da dama a Syria da Iraqi STR / RUSSIAN DEFENCE MINISTRY / AFP
Talla

Rundunar hadin gwiwar ta bayyana a cikin rahoton da ta ke fitarwa duk karshen wata cewa, har yanzu tana kan tantance rahotanni guda biyar da ke nuna kisan da aka yi wa fafaren hula bisa kuskure a yayin yaki da mayakan jihadi a shekarun 2015 da 2016.

Alkaluman da rundunar sojin ta fitar sun sha ban-ban da na wasu kungiyoyin duniya kamar Air Wars, wadda ke sa ido kan kisan da ake yi wa fafaren hula ta hanyar hare-haren sama.

Air Wars ta ce, fararen hula dubu 2 da 100 ne aka hallaka a Iraqi da Syria tun bayan da Amurka ta fara jagorantan hare-haren.

Hukumomin sojin Amurka sun bayyana damuwa game da mutuwar fararen hular, yayin da rundunar ke cewa ta kara samun sabbin rahotanni 16 game da mutuwar wasu fararen hular daban a cikin watan Nuwamban da ya wuce.

Kazalika hukumomin sun ce, suna kan gudanar da bincike game da harin da sojin suka kai kan motar mayakan IS a ranar 29 ga watan Disamba, in da daga bisani aka bayyana cewa motar ta aikin asibiti ne.

Yazuwa karshen watan jiya, kasar Amurka da kawayenta sun kai jumullar hare-hare har dubu 17,005 kan mayakan IS, in da suka kai dubu 10 da 738 a Iraqi, yayin da kuma suka kai sauran dubu 6 da 267 a Syria kamar yadda alkaluman sojin Amurka suka nuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.