Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya sanya hannu kan dokar fidda Amurka daga TPP

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan dokar janye kasar daga yarjejeniyar kasuwancin da aka yiwa lakabi da TPP.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan yarjejeniyar fidda Amurka daga Tsarin TPP
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan yarjejeniyar fidda Amurka daga Tsarin TPP REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Tun kafin rantsar da shi, Trump ya yi alkawarin fitar da kasar daga yarjejeniyar da ta kunshi kasashe irin su Australia da Canada da Japan wadanda ke mamaye da kashi 40 na harkokin kasuwancin duniya.

Bayan soke yarjejeniyar, Trump ya ce zai koma dan tattauna wa da kowacce daga cikin kasashen da ke ciki dan kulla wata sabuwar yarjejeniya tsakanin ta da Amurka.

A wani labarin kuma, wasu Lauyoyi a Amurka sun gurfanar da shugaban kasar Donald Trump a gaban kotu kan tuhumar da suke masa na karba kudade daga gwamnatocin wasu kasashe wanda hakan ya saba dokokin Amurka.

Kungiyar ta ce yanzu haka harkokin kasuwancin shugaban na habaka ne sakamakon kayutatawar da ake masa a matsayin shugaban kasa, wanda hakan laifi ne.

Shugaban kasar ya yi watsi da karar wanda ya bayyana ta a matsayin mara tasiri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.