Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya gayyaci Netanyahu

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce shugaban kasar Amurka Donald Trump ya gayyace shi zuwa birnin Washington domin wata tattaunawa a tsakaninsu.

Shugaban Amurka Donald Trump da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Shugaban Amurka Donald Trump da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu REUTERS
Talla

Wannan ya biyo bayan tattaunawar da suka yi ta waya inda sanarwar ta bayyana cewar shugabannin biyu sun fahimci juna.

Netanyahu ya bayyana aniyarsa na aiki tare da sabon shugaban musamman kan batun tsaron Gabas ta Tsakiya da kuma tabbatar da cewar Iran ba ta mallaki makamin nukiliya ba.

Gwamnatin Isra’ila ta bayar da iznin komawa ga aikin ginin gidajen yahudawa ‘yan kakagida 566 a yankin gabashin birnin kudus, kwana biyu da aka rantsar Donald Trump a wanda ya lashi takobin mayar da ofishin jakadancin Amurka a birnin, domin nuna goyon bayansa ga Isra’ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.