Isa ga babban shafi
Amurka

An dakatar da bin umurnin dokar Trump kan musulmi

Hukumomin Amurka sun dakatar da bin umurnin dokar da Donald Trump ya kafa ta haramtawa wasu ‘yan kasashen musulmi bakwai shiga kasar, bayan wani alkalin kotu ya soke dokar a yau Asabar.

An yi zanga-zangar adawa da manufofin Trump a kasashen duniya
An yi zanga-zangar adawa da manufofin Trump a kasashen duniya Reuters
Talla

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da hukuncin na kotun kasar da ta dakatar da matakinsa na haramtawa wasu kasashe bakwai na musulmi shiga Amurka.

Trump ya rubuta a shafin shi na Twitter cewa zai kalubalanci hukuncin wanda alkalin wata kotun Amurka James Robert ya zartar.
Tuni dai kamfanonin jiragen sama suka sanar da komawa aikin jigilar fasinja a kasashen da Trump ya hana shiga Amurka a makon da ya gabata.

Alkalin kotun ya ce umurnin da Trump ya sanyawa hannu ya saba dokar kasa.

Amma a martanin da ya mayar, shugaba Trump ya ce duk kasar da ba ta iya tantance wanda zai shigo ya fita domin tsaron kasa, matsala ce babba.

Kasashen da haramcin na Trump ya shafa sun hada da Iran da Iraq da Libya da Somalia da Sudan da Syria da kuma Yemen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.