Isa ga babban shafi
Amurka

Babbar Kotun Amurka ta hana aiwatar da matakin koran baki

Wani alkalin kotu a kasar Amurka ya hana aiwatar da umarnin shugaba Donald Trump na hana bakin daga kasashe bakwai na musulmi tsoma kafarsu cikin kasar Amurka al’amarin da ya haifar da zafafan kalamai dan tsakanin nan.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Jonathan
Talla

Alkalin yankin Seattle James Robart ya haramta aiwatar da dokan shugaban kasar ne a fadin Amurka har sai an duba batun koken dake gaban babban mai sharia na Washington Bob Ferguson.

Sai dai wata sanarwa daga Gwamnatin Amurkan na cewa matakin da shugaba Donald Trump ya dauka na kishin kasar ne kuma kundin tsarin mulkin Amurka ya bashi ikon yin haka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.