Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta daukaka kara saboda hana ta koran baki

Ma'aikatar Sharia ta kasar Amurka ta daukaka karar hukuncin da wata kotun kasar ta yanke na yin watsi da matakin hana baki shiga Amurka musamman daga kasashen musulmi bakwai, da Shugaba Donald Trump ya sanar.

Shugaban Amurka Donald Trump a lokacin da yake zartas da hana baki shiga Amurka
Shugaban Amurka Donald Trump a lokacin da yake zartas da hana baki shiga Amurka REUTERS/Carlos Barria
Talla

A ranar Juma'a ne dai wata kotu a Washington ta dakatar da aiwatar da hana bakin shiga Amurka saboda a warware batutuwan da suka shafi sharia.

Dubban mutane daga London , Paris da New York da Washington  sun gudanar da zanga-zangan kyamar matakan na Shugaba Donald Trump na hana baki shiga Amurka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.