Isa ga babban shafi
Amurka

Ko dokar Trump wariya ce ga Musulmi?

Kotun daukaka kara ta Amurka ta gabatar da tambaya don sanin ko dokar hana shigar baki da shugaban kasar Donald Trump ya kafa, wata alama ce da ke nuna wariya ga Musulmin duniya. 

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. Brendan Smialowski / AFP
Talla

Dokar wadda aka dakatar da ita, ta hana kasashen musulmi bakwai shiga cikin kasar ta Amurka na wucen gadi saboda barazanar tsaro kamar yadda gwamnatin Donald Trump ta fadi.

Sai dai a makon jiya ne kotu ta dakatar da dokar, yayin da ta bukaci gwamnatin Trump da ta gabatar da gamsassun hujjoji na daukan wannan mataki.

Wani alkalin kotun daukaka karar kasar Richard Clifton, ya gabatar da tambaya don sanin ko wannan doka za ta iya zama tamkar wariya matukar ta shafi kashi 15 cikin 100 na al’ummar musulmin duniya.

Mr. Clifton na cikin alkalan kotun San Francisco da ake saran za su yanke hukunci kan wannan takardama a cikin wannan makon.

Kasashen Musulmin da dokar ta shafa sun hada da Libya da Yemen da Sudan da Iran da Iraq da Somalia da Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.