Isa ga babban shafi
Amurka

Musulmi na shiga Amurka bayan dakatar da dokar Trump

Matafiya daga kasashe bakwai da Donald Trump ya haramtawa shiga Amurka sun fara isa kasar bayan kotun daukaka kara ta ki dawo da dokar kamar yadda fadar white house ta bukata bayan soke dokar da wani alkalin kotun Washington ya yi.

Musulmi na farin cikin shiga Amurka bayan dakatar da dokar Trump
Musulmi na farin cikin shiga Amurka bayan dakatar da dokar Trump REUTERS
Talla

Babbar kotun Amurka ta bukaci bangaren gwamnatin Trump da kuma jihohin da ke adawa da matakinsa su gabatar da hujjojin da suke dogaro da su akan doka, kafin cikar wa’adin da kotun ta bayar a yau litinin.

‘Yan kasashe bakwai Iran da Iraqi da Syria da Somalia da Libya da kuma Yemen wadanda takardunsu na biza ba su gama aiki ba sun fara isa Amurka bayan soke dokar Trump.

Wasu daga cikin matafiyan sun bayyana farin cikinsu bayan haramta masu shiga Amurka.

Wata daliba daga Iran mai suna Sara tana cikin wadanda dokar Trump ta sa aka mayar da ita kasarta, amma yanzu ta samu isa Los Angeles inda ta godewa alkalan da suka kalubalanci dokar.

Hukumomin Amurka sun ce ‘yan kasashen bakwai na Musulmi da ke da takardu yanzu suna da ‘yancin shiga kasar idan har takardunsu basu gama aiki ba.

Yanzu haka ‘yan kasashen da dama ne ke rige rigen shiga Amurka don gudun abin da zai biyo bayan hukuncin da kotun daukaka kara za ta yanke bayan ta saurari hujjojin doka daga bangaren gwamnatin Trump da kuma alkalan jihohin da ke adawa da matakin.

bizar mutane 60,000 aka soke daga lokacin da Trump ya bayar da umurnin hana shiga Amurka daga kasashen bakwai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.