Isa ga babban shafi
Amurka

Kotu ta ki dawo da dokar Trump ta haramta shiga Amurka

Kotun daukaka kara a Amurka ta yi watsi da bukatar da bangaren shari’ar kasar ya shigar kan gaggauta tabbatar da dokar Donald Trump da ta haramta wa ‘yan kasashen musulmi bakwai shiga kasar, bayan wata kotu a Washington ta soke dokar.

An yi zanga-zangar adawa da manufofin Trump a kasashen duniya
An yi zanga-zangar adawa da manufofin Trump a kasashen duniya REUTERS
Talla

Hakan dai na nufin kotun daukaka karar ta tabbatar da hukuncin da wata kotun ta zartar na soke Dokar Trump ta haramta shiga Amurka daga kasashen bakwai na musulmi.

Alkalai da dama daga jihohin Amurka sun ce dokar ta sabawa kundin tsarin mulki.

Kotun daukaka kara kuma ta ba da wa’adi zuwa gobe Litinin ga bangaren Trump da kuma jihohin da ke adawa da matakin su gabatar hujjoji da suke dogaro akai.

Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a manyan biranen kasashen Turai domin nuna adawa da matakin na Donald Trump

Tun a jiya Asabar mutanen London suka kaddamar da zanga-zangar, kamar yadda daruruwan mutane suka fito a biranen Paris da Washingoton da kuma New York.

Ana zanga-zangar ne domin nuna goyon baya ga kasashen muslmi bakwai da Trump ya haramtawa shiga Amurka na tsawon watanni 3 da suka hada da Iran da Iraq da Libya da Somalia da Sudan da Syria da kuma Yemen.

Sannan Trump haramtawa ‘yan gudun hijira shiga Amurka na tsawon kwanaki 120.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.