Isa ga babban shafi
Amurka

Hoto ya haddasa cece-ku-ce daga White House

Shugaban Amurka Donald Trump ya gana da tsoffin dalibai da Shugabanin makarantun bakaken fata na kasar a fadar sa da ke White House.Ziyarar da ke zuwa a dai dai lokacin da Shugaba kasar Trump ke kokarin sake dawowa da martabarsa ga Amurkawa da kuma sauran kasashen duniya. 

Shugaban Amurka Donald Trump da  tsoffin  dalibai  da Shugabanin makarantun bakaken fata
Shugaban Amurka Donald Trump da tsoffin dalibai da Shugabanin makarantun bakaken fata
Talla

To sai dai a lokacin da shugaban ke daukar hoto da mutanen da ke cikin wannan tawaga da ta ziyarce shi, a lokacin kuwa daya daga cikin masu bai wa Shugaban shawara Kellyane Conway ta kasance zaune kan babbar kujerar fadar White House ba tare da ta cire takalmanta ba.

Wannan hoto dai yanzu haka ya fara haddasa cece-ku-ce a tsakanin al’umma bayan da aka yada shi a shafukan sada zumunta da mahawara. Yayin da wasu ke kallon lamarin a matsayin rashin da’a ga shugaban da kuma bakinsa, yayin da wasu ke cewa Conway ba ta da kwarewa ne a game da aikin da ya rataya a wuyanta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.