Isa ga babban shafi
MDD-Iraq

Dole a kare lafiyar fararen hula- Guterres

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya kai ziyara a Iraqi don ganin halin kuncin da fararen hula ke ciki a Mosul tun bayan da dakarun kasar suka kaddamar da farmakin kwato birnin daga hannun kungiyar ISIS.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Mr. Guterres ya ce dole ne a mayar da hankali kan kare rayukan fararen hula da kuma kai musu dauki cikin gaggawa.

Ziyararsa na zuwa ne a wani matsanancin lokaci da ake kokarin fatattakar ISIS, sannan kuma ga tarin matsalolin jin kai da ke cika wa da jama'a sakamakon yakin da ake gwabzawa.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe fararen hula 300 a cikin wata guda a Mosul, abin da ya sa Majalisar da Amnesty kiran a kare rayukansu.

Babu wadatattun sansanoni ga fararen hula da aka raba da muhallansu.

Hukumomin Iraqi sun ce, fararren hula fiye da dubu 200 ne suka tsere daga Mosul tun bayan kaddamar da farmakin kwato birinin da ya fada a hannun kungiyar ISIS a shekarar 2014.

ISIS dai na iko da yankuna da dama da ke arewa da yammacin Baghdad, sai dai dakarun da ke yaki da su na samun nasara a kansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.