Isa ga babban shafi
Iraqi

MDD da Amnesty sun bukaci kare fararen hula a Mosul

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Amnesty sun bukaci sojojin da ke kai hare-hare Mosul na Iraqi  su tabbatar da kare rayukan fararen hula bayan kashe wasu 300 a kwanakin da suka gabata.

Yakin Kwato Mosul na lakume rayukan fararen hula a cewar Kungiyoyin kare hakkin bil'adama
Yakin Kwato Mosul na lakume rayukan fararen hula a cewar Kungiyoyin kare hakkin bil'adama AHMAD AL-RUBAYE / AFP
Talla

Kakakin ofishin kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya Ravina Shamdasani ta ce tsakanin 17 ga watan Fabarairu zuwa yau an kashe fararen hula sama da 300 a Mosul.

Shugaban Hukumar Zeid Ra’ad Al Hussein ya bukaci sojojin Iraqi da na Amurka da su dauki duk matakan da suka da ce wajen kare rayukan fararen hular.

Sojin hadin kai da ke yaki da kungiyar ISIS a Iraqi ta ce wata kila tana da hannu wajen kashe dimbin fararen hular a Mosul, wanda ya gamu da suka daga sassan duniya.

Janar Stephen Townsend, kwamandan dakarun Amurka da ke yaki da ISIS, ya ce lallai akwai alamun cewar suna da hannu wajen kashe fararen hular da suka mutu sakamakon harin sama.

Sai dai jami’in ya ce ba da gangan suka kai hari akan su ba.

Ita ma Donatella Rovera ta Amnesty ta ce bayanan da suka tattara sun nuna yadda ake kashe fararen hula ba tare da kakautawa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.