Birtaniya da Amurka sun bankado shirin Boko Haram na Sace 'yan Kasashen Waje dake Najeriya
Kasar Birtaniya da Amurka sun sanar da gano yunkurin kungiyar Boko Haram na fara satan baki ‘yan kasashen waje suna garkuwa da su a yankunan Arewa maso gabashin Najeriya.
Wallafawa ranar:
A cewar ofishin kula da harkokin waje na London, sun sami wasu gamsassun bayanai dake nuna ‘yan kungiyar Boko Haram na shirin sace ‘yan kasashen waje dake karamar Hukumar Bama na jihar Borno dake kusa da kasar Kamaru.
Ofishin jakadancin Amurka dake Abuja ya bayyana cewa Amurkawa dake wannan yanki su yi hattara.
‘Yan wannan kungiya ta Boko Haram sun sha sace mutane da suka hada da mata da yara kanana daga wannan yanki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu