Isa ga babban shafi
Faransa

Handicap International ta bukaci haramta amfani da nau'in Bom mai 'ya'ya

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Handicap International ta bukaci kasashen duniya su samar da dokar haramta amfani da nau’in Bom mai ‘ya’ya tare da daukar tsauraran matakai don kawo karshen amfani da shi. Rahoton da kungiyar ta fitar a yau ya nuna cewa an samu karuwar mutanen da nau’in bom din ya illata da ya rubanya adadin na shekarar 2015 da 2016.

Wani yanki na birnin Sana'a da hare-haren Bomb ya lalata a ranar 25 ga watan Agustan 2017.
Wani yanki na birnin Sana'a da hare-haren Bomb ya lalata a ranar 25 ga watan Agustan 2017. REUTERS/Khaled Abdullah
Talla

A cewar rahoton adadin wadanda bom din  ya kashe ko ya illata ya haura fiye da ninkin na shekarun 2015 da 2016, inda ya ce akwai mutum 971 a bara sama da ninkin na shekarar 2015 da aka samu mutum 419 da suka jikkata sanadiyyar nau’in Bomb din.

Rahoton ya ci gaba da cewa akasarin wadanda nau’in bom din ya illata fararen hula ne da kimanin kaso 98 cikin dari.

Rahoton ya ce tun bayan barkewar rikicin Syria a shekarar 2012 ne ake ci gaba da amfani da nau’in Bomb din a kasar, lamarin daya sa kimanin mutum 860 suka jikkata a Syria kadai cikin mutum 971 da suka illata sanadiyyar Bomb din a duniya baki daya a shekarar 2016.

Haka kuma akwai mutum 51 da nau’in Bomb din na ya illata a Laos da kuma mutum 38 a Yemen.

Yanzu haka dai a cewar rahoton kasashe bakwai ne suka yi amfani da nau’in Bomb din mai ‘ya’ya tun daga watan Janairun shekarar 2015, bayan kasashen Syria da Yemen akwai rahotanni da ke nuna cewa anyi amfani da nau’in Bomb din mai ‘ya’ya a yankin Nagorno-Karabakh, yayin wata takaddama da ta faru tsakanin Armenia da Azerbaijan.

Haka kuma a rikicin Somalia ma rahoton ya ce anyi amfani da nau’in Bomb din a 2016 yayinda kasashen Ukraine, Sudan and Libya suka yi amfani da shi a shekarar 2015.

Rahoton ya kuma ce wasu bayanai da ba su da cikakken sahihanci sun nuna cewa an yi amfani da nau’in Bomb din a kasashen Libya da Iraq a 2016 da farko farkon 2017.

A cewar Daraktan wayar da kai da hulda da jama’a na kungiyar Anne Hery ci gaba da amfanin da nau’in Bomb din ya saba ka’idojin yaki na duniya la’akari da yadda ake amfani da shi kan farafen hula, a don haka wajibi ne ayi amfani da dokokin duniya da suka haramta hakan.

Kungiya ta kuma bukaci kasashen da su ke da wadanda suka jikkata sanadiyyar Bom din da su samar da wani shirin tallafawa rayuwar wadanda bom din ya illata ganin yadda kulawarsu ke da wahala, lamarin da ke hana su samun damar ci gaba da gudanar da al’amuransu kamar a baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.