Isa ga babban shafi
Isra'ila

Falasdinawa na neman a janye batun mayar da Kudus babban birnin Isra'ila

Shugabannin Falasdinawa sun gudanar da wani taron gangamin da ya bukaci Shugaban Amurka Donald Trump janye matakin da ya dauka na tabbatar da birnin kudus a matsayin babban birnin kasar Isra’ila.

Harabar Masallacin Kudus mai tsarki
Harabar Masallacin Kudus mai tsarki REUTERS/Muammar Awad
Talla

Mashawarcin shugaban Falasdinawa kan harkokin kasashen waje ya ce Mahmud Abbas ya tattauna da shugabannin duniya domin nuna musu matsalar ko kuma hadarin da ke tattare da mayar da birinin na Kudus babban birnin Isra’ila.

A ranar Laraba mai zuwa ake tunanin shugaban na Amurka Donald Trump zai sanar da mayar da birnin Kudus babban birnin Isra'ila.

Wannan dai ba shi ne karon farko da wani shugaban Amurka ya yi yunkurin mayar da Kudus babban birnin Isra'ila ba, sai a wannan lokaci karkashi shugaba Trump  Amurka  ta dage wajen tabbatar da birnin na Kudus ya zama babban birnin kasar ta Isra'ila.

Wasu masharhanta sun bayyana cewa, mayar da birnin na Kudus ga hannun Isra'ila ka iya haifar da tsaiko ga yunkurin  da ake na samar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.

Shugabannin yankin gabas ta tsakiya na ci gaba da yin kiraye-kiraye tare da nuna irin barnar da hakan zai haifar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.