Isa ga babban shafi
Israel-Palestine

Isra'ila ta janye na'urar gano karfe a Masallacin Kudus

Isra’ila ta janye na’urorin shinshinan karafa da ta kafa a Masallacin Haram al-Sharif na birnin Kudus, kuma ta ce, ba za a kara amfani da na’urorin ba sakamakon rikicin da suka haifar da ya yi sanadiyar mutuwar Falasdinawa biyar da Yahudawa uku.

Sabon rikicin ya yi sanadiyar mutuwar Falasdinawa biyar da kuma Yahudawa uku
Sabon rikicin ya yi sanadiyar mutuwar Falasdinawa biyar da kuma Yahudawa uku REUTERS/Ammar Awad
Talla

Matakin janye na’urorin daga Masallacin birnin Kudus na zuwa ne bayan kasashen duniya sun bukaci kawo karshen rikicin, wanda su ka gargadi cewa, ka iya yin kamari ta yadda zai zarce iyakokin Isra’ila da Falasdinu.

A sanyin safiyar yau ne, wata tawagar ma’aikata ta fara katse na’urorin kamar yadda wakilin Kamfanin Dillacin Labaran Faransa na AFP ya rawaito.

Kazalika, shugabannin al’ummar Musulmin yankin sun tabbatar da katse na’urorin na gano karafan da aka boye a jiki.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ta ce, a halin yanzu, Majalisar tsaron kasar ta amince a samar da wasu sabbin matakan sa ido a Masallacin na Haram al-Sherif da Yahudawa ke kira Temple Mount bayan janye wadannan na’urori.

Sai dai kawo yanzu babu tabbaci kan ko Musulmai za su amince da sabbin matakan tsaro a Masallacin.

A bangare guda, shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya bukaci Musulman duniya da su ziyarci birnin Kudus bayan wannan rikici da ya barke tsakanin Falasdinawa da Yahudawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.