Isa ga babban shafi
Duniya

Mike Pence ya kauracewa hada zama da Kim Yon Naam

Mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence ya kauracewa zama teburi guda da shugaban gwamnatin jeka nayi ka a Korea ta arewa Kin Yon Naam , a wani zaman cin abincin dare da ya hada su lokacin bikin bude gasar Olympics  a pyeongchang.A bangare guda kuma yayin cin abincin an gaisa tsakanin yar uwar shugaban koriya ta arewan da shugaban kasar korea ta kudu Moon Jae In, awani yanayi mai cike da tarihi da aka jima ba’a gani ba.

Tuni dai fadar gwamnatin Korea ta kudun Blue house ta wanke Mr Pence inda ta ce rashin halarta ta sa na da nasaba da makarar da ya yi zuwa wurin cin abincin.
Tuni dai fadar gwamnatin Korea ta kudun Blue house ta wanke Mr Pence inda ta ce rashin halarta ta sa na da nasaba da makarar da ya yi zuwa wurin cin abincin. 路透社。
Talla

Tun da fari dai an shirya zaman ne wuri guda tsakanin shugaban jeka nayi kan Korea ta arewan Kim Yon Naam, tare da shugaban korea ta kudu moon jae in da kuma mataimakin shugaban Amurkan Mike Pence, kuma tsarin zaman anan kallon juna na ne tsakanin Mr Pence da Kim, amma sai Mr pence ya kauracewa zaman bayan gaisuwar daga hannu.

Ko da dai fadar gwamnatin Korea ta kudun Blue house ta wanke Mr Pence inda ta ce rashin halarta ta sa na da nasaba da makarar da ya yi zuwa wurin cin abincin.

Kasashen Korea ta kudu ta Korea ta Arewan sun kafa tarihin gaisawa cikin raha tsakanin yar uwar shugaban korea ta arewa Kim yo Jong da shugaba Moon jae In, yayin bikin bude gasar ta Olympics bayan shafe tsawon shekaru suna gaba da juna.

Rabon dai da wani shugaba daga jamiyyar Dynasty da ke mulkin Korea ta arewa ya ziyarci kudancin tun cikin shekarar 1953, bayan kammala yakin basasar yankin.

Manazarta dai na ganin watakila danganta ta dawo tsakanin kasashen biyu sanadiyyar wasannin na Olympcs la'akari da yadda suke tafiyar da al'amuransu cikin walwala da kaunar juna.

Kasashen biyu dai sun yi tattaki lokacin bikin bude gasar a safiyar yau cikin launin tutocin su na shudi da fari cikin wani yanayi mai kawatarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.