Isa ga babban shafi
Rasha

Rasha za ta rage kasafin kudin bangaren aikin soji

Shugaba Vladimir Putin, ya yi alkawarin rage kudaden da kasar ta Rasha ke kashewa a bangaren aikin soji, kwana daya bayan da ya yi nasara a zaben shugabancin kasar.

Shugaban na Rasha da ya samu damar zarcewa a shugabancin kasar har zagaye na hudu ya sha alwashin kawo karshen takaddamar da ke tsakaninsa da kasashen duniya ta hanyar Diflomasiyya.
Shugaban na Rasha da ya samu damar zarcewa a shugabancin kasar har zagaye na hudu ya sha alwashin kawo karshen takaddamar da ke tsakaninsa da kasashen duniya ta hanyar Diflomasiyya. Yuri Kadobnov/POOL via Reuters
Talla

Putin, wanda ke gabatar da jawabi a gaban sauran ‘yan takarar da suka kara da shi a zaben na jiya, inda ya ce Rasha ba ta da niyyar sake shiga gasar kera makamai da wata kasa ta duniya.

Ana dai kallon kalaman na Putin a matsayin martini kan matakin shugaban Amurka Donald Trump wanda ya kaddamar da wani sabon shirin bunkasa bngaren nukiliyar kasar a watan jiya.

Yanzu haka dai Putin na fuskantar mabanbantan kalubale musamman a bangaren da suka shafi zarginsa da katsalandan a rikicin Ukraine da Syria baya ga wani zargin kutsen na daban kan zaben Amurka na 2015 da kuma na baya-bayan nan zargin amfani da makami mai guba kan tsohon dan leken asirin Rashan da ke aiki da Birtaniya.

Sai dai cikin Jawaban na sa, Vladimir Putin ya ce baya fatan dorewar rikicin da ke tsakanin kasarsa da kasashen duniya, hasalima yana fatan warwarewar rikicin ta hanyar diflomasiyya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.