Isa ga babban shafi
Rasha-Birtaniya

Rasha ta kori jam’ian Diflomasiyyar Britaniya

Kasar Rasha ta bayyana korar jamian ofishin yada al’adu da ilimi na kasar Britaniya  su 23 da ke kasar a matsayin martini kan matakin da Britaniyar ta dauka na korar jami’an jakadancinta.Sabani tsakanin kasashen biyu na zuwa ne tun bayan wani kisan gilla da ita Birtaniyar ke zargin Rasha da aikatawa kan tsohon dan leken asirinta da ya koma yiwa Birtaniyar aiki a yanzu tare da 'Yarsa ta hanyar amfani da wani sinadarin guba mai hadari. 

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin. Reuters
Talla

Cikin martinin na Rasha da ake kallo da mafi muni kan matakin Birtaniya, ya sanar da cewa dama Ofishin yada al’adu da ilimi na kasar Britaniya da ke kasarta, ba ya a kan ka’ida don haka daga yau sun kawo karshen aikinsa a kasar.

Tsamin dangantaka tsakanin Rasha da manyan kasashen yammacin Turai da Amurka ya kara rincabewa ne tun bayan da ita Rashan ta tsunduma hannu a rikice-rikicen kasashen Ukraine da Georgia da ke makwabtaka da ita, kasashen da ke da  matukar muhimmanci ga Amruka da Turai ta fannin tsaro, da kuma samun damar kutsa kai a yankunan da Rashan ke makwabata da su, ko da ya ke ita Rashan na kallon batun a matsayin barazanar ga tsaronta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.