Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta jajantawa Faransa kan harin jiya

Shugaban Amurka Donald Trump ya jajantawa Faransa kan harin jiya da ya hallaka mutane hudu baya ga Jami'in dan sandan da ya mutu yau daga baya.

Shugaban na Amurka Donald Trump ya kuma bayyana cewa suna tare da Emmanuel Macron a yakin da ya ke da ta'addanci.
Shugaban na Amurka Donald Trump ya kuma bayyana cewa suna tare da Emmanuel Macron a yakin da ya ke da ta'addanci. REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Trump a sakon Twitter da ya aike ya yaba da kwazon jami’in Dan sandan wanda ya bayar da rayuwarsa don ceto al’ummar kasar da dan bindigan ya yi garkuwa da su tun da farko, yayin da ya yi fatan samun sauki ga daukacin wadanda harin ya jikkata.

Sakon na Donald Trump ya ci gaba da cewa basa goyon bayan duk wani ayyukan ta’addanci inda ya ce yana tare da shugaba Emmanuel Macron.

Da tsakar ranar jiya Juma’a ne dai maharin dan shekaru 25 da aka bayyana sunanshi da Redouane Lakdim da ya yi ikirarin cewa shi dan kungiyar IS ne ya kwace wata motar Tasi a Carcassonne tare da hallaka matukin da kuma harbin fasinjan da ke ciki kafin daga bisani ya tinkari wani shagon sayar da kayaki a Trebes inda ya yi garkuwa da mutanen da ke ciki bayan hallaka mai shagon da kuma wani mutum guda.

Laftanal Kanal Arnaud Beltrame shi ne jami’in dan sandan da ya yi musayar kansa da mutanen da dan bindigar ya yi garkuwa da su lokacin da maharin ya yi yunkurin fara yin dauki dai dai ga daukacin masu sayen kaya da ke shagon.

Lakdim dai ya harbi Kanal Beltrame tare da soka mishi wuka a yammacin na jiya kafin daga bisani ya mutu a safiyar yau asabar.

Tuni dai shugaban kasar Emmanuel Macron ya bayyana Kanal Beltrame a matsayin gwarzo mai kishin al’ummarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.