Amurka da wasu kasashen Turai sun kori jakadun Rasha
Bisa umurnin Shugaban amurka Donald Trump Amurka ta kori jakadun Rasha 60 daga kasar, a matsayin maida martani ga harin gubar da ake zargin Rashan da kaiwa Serguei Skripal tsohon jami’in leken asirin Rashan mazaunin Britaniya.A matsayin goyan baya wasu kasashen Turai da dama sun dauki matakan sallamar jakadun Rashan a yau Litinin.
Wallafawa ranar:
Sarah Sanders dake magana daga fadar Gwamnatin Amurka tace matakin na a matsayin martani ga Moscow, bisa harin sinadarin gubar da ake zargin ta da kaiwa.
Yanzu haka dai wa’adin kwanakin bakwai aka baiwa jakadun kan cewa sun bar kasar.
Tuni dai itama kungiyar tarayyar turai ta ce komai ya kammala na katse duk wata hulda da Rashan, bayanda ta kira jakadanta dake Moscow
kasashen turai shida ne yanzu haka suka soma daukar matakin,Ukrain, Polan, bayaga wasu daga yankin balkan irinsu Lithuania,da Estonia
Tuni itama kasar Canada tabi sahu, inda ta bayyana batun harin gubar da aikin asha,
Faransa da Jamus sun fito fili tareda sanar da korar jakadun rasha 4 daga kasashen su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu