Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

kotun kolin Brazil ta tabbatar da hukumcin daurin shekaru 12 ga tsohon shugaban kasar Lula...

Wallafawa ranar:

Kotun kolin kasar Brazil ta bada umarnin aikin da hukumcin daurin shekaru 12 da aka zartar kan tsohon shugaban kasar Lula de Silva na jefa shi a gidan yari, bayan da kotun ta yi watsi da karar da ya daukaka a gabanta yana mai kalubalantar hukuncin daurin shekaru 12 da wata daya da wata kotun ta yanke ma sa, saboda samun sa da laifin karbar ginannen gida daga wani kamfani, a matsayin rashawa.Lula mai shekaru 72 a duniya, ya taka gagarumar rawa wajen samar wa kasar Brazil cigaban tattalin arzikin da take tinkaho da shi a yau.Moussa Aksar, mai sharhi kan lamurran yau da kullum daga jamhuriyar Nijer, ya bayyana hukuncin a matsayin galaba ga dimokuradiyya.

Tsohon shugaban kasar Brazil  Lula da Silva
Tsohon shugaban kasar Brazil Lula da Silva REUTERS/Leonardo Benassatto
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.