Isa ga babban shafi
Brazil

Shugaban Brazil ya tsallake yunkurin dakatar da shi

Yunkurin da 'yan majalisa suka yi domin dakatar da shugaban Michel Temer na Brazil wanda ake zargi da rashawa ya ci tura, inda aka gaza samun adadin 'yan majalisar da ake bukata kafin tabbatar da yunkurin.

Majalisar wakilan Brazil na muhawara kan tsige Shugaba Michel Temer
Majalisar wakilan Brazil na muhawara kan tsige Shugaba Michel Temer REUTERS/Marcos Brindicci
Talla

‘Yan adawa sun yi ta yin ba’a ga shugaban, in da suka yi ta kai kawo da akwatina kwa-tan-kwa-cin wanda wani mai taimakawa Temer ya riko lokacin da aka kama shi dauke da Dalar Amurka dubu 150 a matsayin na goro ga mai gidansa kamar yadda aka zarga.

‘Yan adawa sun yi ta daga murya a zauren Majalisar, in da suke cewa, a yi waje da Temer.

Ana zargin shugaban da karban cin hancin daga shugaban wani kamfanin kula da tsaftar naman dabbobi a kasar.

Da zarar, kashi biyu bisa uku na mambobin Majalisar sun amince da tuhumar shugaba Temer, to lallai, dole ne a dakatar da shi daga kujerarsa har na tsawon kawanaki 180 don amsa tambayoyi a gaban Kotun Kolin kasar.

Sabuwar badakalar na zuwa ne bayan watanni 12 da Majalisar kasar ta tsige tsohuwar shugabar kasar Dilma Rousseff saboda al’mundahana.

Sai dai wasu masu sharhin na cewa, watakila shugaba Temer ya tsallake rijiya da baya, domin kuwa yana iya samun goyon baya daga akasarin ‘yan Majalisar da yawansu ya kai 342.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.