Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

'Yan Afrika miliyan 17 sun fice daga nahiyar a bara - Rahoto

Wani Rahotan Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewar akalla Yan kasashen Afirka miliyan 17 suka fice daga kasar a shekarar 2017 domin neman rayuwa mai inganci a sassan duniya.

Rahotan ya ce gaba daya mutane miliyan 19 ne suka sauya wuri daga Afirka, banda wadanda suka fice daga cikin nahiyar baki daya.
Rahotan ya ce gaba daya mutane miliyan 19 ne suka sauya wuri daga Afirka, banda wadanda suka fice daga cikin nahiyar baki daya. NAN
Talla

Wannan rahoto da aka gabatar da shi a taron Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kasuwanci da kuma cigaba, ya ce yayin da Yan Afirka miliyan 17 suka bar nahiyar su, wasu yan kasashen duniya miliyan 5 da rabi suka sheka nahiyar domin gudanar da harkokin su na yau da kullum.

Rahotan ya ce gaba daya mutane miliyan 19 ne suka sauya wuri daga Afirka, banda wadanda suka fice daga cikin nahiyar baki daya.

Sakatare Janar na Hukumar Cinikayya da kuma cigaba Mukhisa Kituyi ya ce an samu karuwar kudaden da baki yan cirani da suka bar Afirka su ke aikewa gida daga Dala biliyan 38 da kusan rabi tsakanin shekarar 2005 zuwa 2007 zuwa Dala biliyan 65 zuwa shekarar 2016.

Sakataren ya ce Yan kasar Cote d’Ivoire dake kasashen waje ke samar da kashi 20 na kudin da kasar ke samu daga shekara 2008, yayin da Rwanda ke samun kashi 13.

Junior Davis, wanda ya jagoranci rubuta binciken da aka gudanar a wajen taron, yace Afirka ta kama hanyar samun cigaba mai dorewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.