Isa ga babban shafi
Saudi-Yemen

Dakarun hadaka na Saudiyya na luguden wuta a Hodeida

A rana ta biyu da dakarun kawancen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya suka kaddamar da farmaki domin sake kwato garin Hodeida mai tashar jiraren ruwa daga ‘yan tawayen Huthi, rahotanni sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 39 mafi yawansu fararen hula a yau alhamis.

An ci gaba da gwabza fadan ne a dai dai lokacin da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ke gudanar da zama na musamman a asirce dangane da halin da ake ciki a kasar ta Yemen biyo bayan kaddamar da wannan farmaki.
An ci gaba da gwabza fadan ne a dai dai lokacin da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ke gudanar da zama na musamman a asirce dangane da halin da ake ciki a kasar ta Yemen biyo bayan kaddamar da wannan farmaki. Reuters
Talla

Dakarun Yemen wadanda ke samun goyon bayan sojoji daga kasashen larabawa ne suka kaddamar da farmakin a jiya, a matsayin wani yunkuri na karbe birnin na Hodeida wanda ‘yan tawayen Huthi masu samun goyon bayan Iran ke iko da shi da kuma Sanaa yau shekaru uku kenan.

Rahotanni sun tabbatar da cewa dakarun kawance dauke da manyan makamai tare da rakiyar jiragen yaki sun barin wuta a kan birnin, ciki har da unguwannin da mafi yawan mazaunansu fararen hula ne, to sai dai tabbas suna fuskantar turjiya daga ‘yan tawayen

An ci gaba da gwabza fadan ne a dai dai lokacin da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ke gudanar da zama na musamman a asirce dangane da halin da ake ciki a kasar ta Yemen biyo bayan kaddamar da wannan farmaki.

Sweden, kasar da ba ta da kujerar dindindin amma ta nemi Kwamitin tsaron da ya samar da kudurin da zai tilasta wa bangarorin da ke da hannu a rikicin tsagaita wutar domin bayar da damar isar da kayayyakin jinkai ga dubban mutanen da ke yankin na Hodeida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.