Isa ga babban shafi
Amurka

Obama da George Bush za su halarci jana'izar John McCain

A yau asabar aka soma jana’izar dan majalisa kuma tsohon dan takarar zaben Shugabancin Amurka John McCain da ya rasu ya na mai shekaru 81.Dubban jama’a ne suka halara a babbar mujami’ar dake Washington domin yi masa bankwana, inda ake sa ran tsoffin Shugabanin kasar George Bush da Barack Obama za su gabatar da jawabi kamar dai yadda mamacin ya bukaci a yi .

Jana'izar John McCain  a Amurka
Jana'izar John McCain a Amurka REUTERS/Kham
Talla

Sanata John McCain, matukin jirgin saman yaki da aka azabtar a lokacin yakin Vietnam, haka kuma dan takarar shugabancin kasar Amruka ya rasu yana dan shekaru 81 a duniya, sakamakon cutar sankarar kwakwalwa da ya yi fama da ita.

Ofishin sanatan na jam’iyar Republicain ya sanar da cewa, kafin mutuwarsa Marigayin dai ya bautawa kasar Amruka na tsarwon shekaru 60

Dan takarar da ya sha kaye a zaben shugabancin kasar Amruka na shekara ta 2008 da Barack Obama ya lashe, na dauke ne nakasar wani sashen jiki da ya samu, a yakin Vietnam, sakamakon raunukan da ba a warkar da kyau ba, da kuma a zabar da ya sha a kurkuku.

A ranar 26 ga watan Oktobar 1967, ne makamin sol-air kirar kasar Rasha ya kakkabo jirgin yakin da yake tukawa kirar A-4 Skyhawk a sararin samaniyar garin Hanoï na kasar Vietnam.

McCain ya fitar da kansa ta rigar lema daga jirgin, inda ya fado a tsakiyar kogin garin, jifar da jama’a suka yi masa ce, ta yi sanadiyar kaririyar hannayensa biyu da gwiwar hannunsa ta dama.

Ba a gayyaci Shugaban Amurka Donald Trump a jana’izar John McCain dake gudana a yau .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.