Isa ga babban shafi
Amurka

An kai harin bindiga kan dandazon jama'a a Amurka

Mutane da dama sun rasa rayukansu, yayin da wasu suka jikkata sakamakon wani harin bindiga da aka kaddamar a ginin ma’ajiyar kayayyaki da ke arewacin Baltimore na Amurka.

Ana yawan fama da hare-haren bindiga kan mai uwa da wabi a Amurka
Ana yawan fama da hare-haren bindiga kan mai uwa da wabi a Amurka DOMINICK REUTER / AFP
Talla

Rahotanni na cewa, wata mace ce ta kaddamar da harin bindigar kan dandazon jama’a, abin da ba a saba gani ba a kasar cewa, mace ta kai irin wannan farmakin.

Ko da dai jami’an ‘yan sanda na kan aikin tantance hakikanin jinsin maharin ko kuma ‘yar bindigar.

Shugaban rundunar ‘yan sandan yankin Harford da ke Maryland, Jefferey Gahler ya tabbatar da jikkatar mutane da dama da kuma salwantar rayuka.

Gahler ya ce, ana ci gaba da tsare ‘yar bindigar daya tilo wadda ke cikin mawuyacin hali a wani karamin asibiti.

Jami’in ya ce, akwai yiwuwar matar ce ta raunata kanta da kanta domin kuwa babu wani dan sanda da ya yi harbi da nufin martani ga harin.

Kafofin yada labaran Amurka sun rawaito cewa, akalla mutane uku aka rasa a harin wanda aka kai a cibiyar rarraba magunguna ta Rite Aid da ke ginin na ma’ajiyar kayayyaki.

Tuni aka baza jami’an Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka FBI a wurin da harin ya auku.

Ana yawaitar samun hare-haren bindiga kan dandazon al’umma a Amurka, yayin da kundin tsarin mulkin kasar ke kare hakkin mallakar bindigar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.