Isa ga babban shafi
Amurka

An kai harin bindiga a gidan rawa da ke Florida

Jami’an ‘yan sandan Amurka sun tabbatar da mutuwar mutane biyu da kuma raunana 16 a harin bindigar da aka kai wani gidan rawa da ke birnin Fort Myers na jihar Florida.

Akalla mutane biyu ne suka rasa rayukansu a harin bindigar da aka kaddamar a gidan rawar Club Blu da ke Florida ta Amurka
Akalla mutane biyu ne suka rasa rayukansu a harin bindigar da aka kaddamar a gidan rawar Club Blu da ke Florida ta Amurka Captura de vídeo 7NEWS
Talla

An kaddamar da harin ne da misalin karfe 12:30 na daren da ya gabata kuma a daidai lokacin da gungun matasa ke taron shagali a gidan rawar na Club Blu.

Sanarwar da jami’an ‘yan sandan suka fitar ta ce, wadanda suka samu raunukan na kwance a  asibiti kuma wasu daga cikin su na fuskantar barazanar rasa rayukansu.

Jami’an ‘yan sandan na kokarin gano makasudin kaddamar da harin duk da cewa an kama mutane uku sakamakon aukuwar lamarin.

Sabon harin na zuwa ne bayan makwanni shida da wani matashi mai suna Omar Mateen ya hallaka mutane 49 a harin bindigar da ya kai wani gidan rawa na ‘yan luwadi da madigo a Orlando.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.