Isa ga babban shafi
Findland-Tattalin arziki

Ilahirin gwamnatin Firaminista Juha Sipila na Finland ta yi murabus

Firaministan kasar Finland Juha Sipila ya mika takardar murabus din ilahirin gwamnatinsa, da ya shafi baki dayan mukarabbansa da shi kansa, a wanna Juma’a. Matakin Firaministan ya biyo bayan rashin karbuwar kudurinsa na yi wa sashin lafiya da walwalar ‘yan kasar garambawul.

Firaminista Juha Sipila na Finland da ya sanar da murabus din ilahirin gwamnatinsa bayan matakin kin amincewa da kudirinsa na yin garambawul a wasu bangarorin gudanarwar kasar
Firaminista Juha Sipila na Finland da ya sanar da murabus din ilahirin gwamnatinsa bayan matakin kin amincewa da kudirinsa na yin garambawul a wasu bangarorin gudanarwar kasar REUTERS/Vesa Moilanen/Lehtikuva
Talla

Murabus din Firaminista Sipila ya zo ne yayinda da kasar ta Finland ke shirin gudanar da zaben ‘yan majalisu a ranar 14 ga watan Afrilu.

Shugaban Jamhuriyar ta Finland Sauli Ninisto ya amince da murabus din Firaministan kasar, sai dai ya ce Sipila da mukarraban na sa za su ci gaba da rikon kwarya, har zuwa lokacin da za a kafa sabuwar gwamnati.

Sipila wanda shahararren attajiri ne a fannin da ya shafi hada-hadar fasahar sadarwa, ya sanya burin yi wa sashin kula da lafiya da walwalar ‘yan Finland garambawul a matsayin daya daga cikin manufofinsa da ke kan gaba, bayan karbar mukamin Firaminista a shekarar 2015.

Manufar garambawul din kuma shi ne rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa a matsayi tallafi ga ‘yan kasar don kula da lafiyarsu, matakin da zai fi shafar masu yawan shekaru da suka kama da 65 zuwa sama.

Gwamnatocin kasar ta Finland a shekarun baya ma sun sha yin kokarin aiwatar da wannan shiri, amma abin ya faskara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.