Isa ga babban shafi
Finland

Mabiya na ficewa mujami’ar St Lutheran a Finland

Akalla mabiya mujami’ar St Lutheran 13,000 a kasar Finland suka janye daga mujami’ar a cikin kwanaki uku bayan jagoransu ya amince da auran jinsi guda da ake neman halattawa a cikin kasar.

Birnin  Joensuun a kasar Finland
Birnin Joensuun a kasar Finland Tuohirulla / Wikipedia
Talla

Shugaban Mujami’ar ta St Lutheren, Archbishop Kari Makinen ya bayyana farin cikinsa da matsayin majalisar kasar na amincewa da auran jinsi guda a ranar juma’ar da ta gabata.

Rahotanni sun ce daga ranar juma’ar da Archbishop Makinen ya bayyana matsayinsa zuwa jiya litinin mutane 13,000 suka fice daga Cocin don nuna adawa da matakin.

Wannan ya nuna cewar mutanen ba za su biya harajin da suke bai wa cocin ba wanda ake tarawa don aiki da shi.

Sai dai wani babban jami’in mujami’ar Jukka Keskitalo yace kuri’ar da majalisar ta yi bai sake matsayin cocin ba akan auran jinsi guda.

Kashi 75 na al’ummar kasar dai mabiya mujami’ar St Lutheren ne a kasar ta Finland.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.